Nigerian Red Cross Society ta yi gwaje-gwajen cututtuka da bada magunguna kyau ta mutane dubu 1,500 a ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƙungiyar ta yi taron ne a asibitin mata na Dala a ranar Alhamis domin bikin zagayowar ranar Red Cross na 2026, wanda ake yi a duk ranar 8 ga watan Mayu.
Da ya ke jawabi ga manema labarai, babban Sakataren ƙungiyar, reshen jihar Kano, Alhaji Musa Abdullahi ya ce mutane 1,500 su ka amfana da gwaje-gwajen cututtuka daban-daban da kuma magunguna kyauta.
Karata:Hukumar SUBEB ta nesanta kanta gaga zargin karɓar kuɗi domin daukar malamai a Bauchi
A cewar sa, Red Cross ta samar da kayan gwaje-gwaje da magunguna kyauta ga waɗanda su ka amfana da shirin.
Ya yi bayanin cewa an yi gwaje-gwaje cututtuka da su ka haɗa da na ciwon hanta ga mutane 200, sai gwajin ƙwayoyin halittar ɗan adam (genotype) ga mutane 100, sai kuma gwajin maleriya ga mutane 200 gami da na tarin fuka (tuberculosis) ga mutane 1,000.
Abdullahi ya kara da cewa an kuma yi gwajin ido da bada gilashi kyauta ga mutane 100 da haɗin gwiwa da ƙungiyar Maisha Meds, inda ya kara da cewa an kuma yi gwajin cutar ciwon suga (diabetes).
Ya kara da cewa Red Cross za ta fadada wannan shiri ga sauran ƙananan hukumomin jihar nan gaba.
