Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ta ɓullo da wani tsarin na auna ingancin littattafan karatun da ake amfani da su a firamare da ƙaramar sakandare da babbar sakandare a matsayin wata haya ta tabbatar da inganci ilimi a Najeriya.
Ana sa ran fara amfani da tsarin ne a watan Satumba kuma iya littattafan da auna ingancinsu kuma suka tsallake tantance a matsakin ƙasa ne za a amince a yi amfani da su.
A cikin jawabin da ya fitar a ranar Litinin, mai magana da yawun dda yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ya ce, za a fara amfani da tsarin ne bayan kafa kwamitin da fidda tsarin tantancewar.
A cikin jawabin, an bayyana cewa an ɓullo da tsarin ne domin magance yawan littattafai barkatai da tabbatar da ingancinsu da bin tsarin manhajar karatu da ake amfani da su a azuzuwa.
An kuma rawaito ministan ilimi, Tunji Alausa, yana cewa sabon tsarin zai ƙarfafa rawar da cibiyar bincike ta ilimi da kawo cigaba (NERDC) ke takawa wacce ke da alhakin amincewa da littattafai da ake koyarwa a makarantu.
Game da sabon tsarin:
A baya, makarantu na iya amfani da kowanne littafin karatu (textbooks) da hukumar NERDC ta amince da shi da sahalewar mawallafin.
Karanta:Gwamna Abba ya magantu kan zargin rabon tallafin “dan kamfai” ga mata a lokacin ziyarar Remi Tinubu
Sai dai NERDC a yanzu za ta riƙa tantance littattafan ta bin wani tsari domin gano wanda ya fi dacewa ga kowanne darashi da matakin karatu.
Haka kuma iya littattafan da suka samu amincewar NERDC kaɗai za a yarda a yi amfani da su a makarantu.
“Biyo bayan tantacewar, wasu littattafan karatu da aka duba ingancinsu aka amince da su domin amfani a makaranta ga kowanne darasi ne za a yi amfani da su a makarantu domin tabbatar ingancinsu ta amfani da su wajen koyo da koyarwa a faɗin ƙasar nan,” ya faɗa.
Ministan ya ce, za a kafa kwamiti wanda zai ƙunshi ƙwararru a ɓangarori daban-daban domin duba littattafan da mawallafa suka miƙa ta la’akari da tsarin koyarwa.
Haka kuma, ma’aikatar ta ce sabon tsarin zai rage yawan adadin littattafan da ake amfani da su da samar da tsayayyun littattafan koyo da koyarwa a makarantu.
Ma’aikatar ta ce za ta wayar da kan malamai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sun fahimci tsarin da kuma bin sa sau da ƙafa.
Recent:Yan bindiga sun kashe mutum hudu ‘yan gida daya a jihar Filato
