<strong>Sabbin bayanai daga Hukumar Kula da harkokin mai ta Najeriya (NMDPRA) sun nuna cewa matatar Dangote ta fitar da kimanin lita biliyan 1.66 na mai da dangoginsa a watan Afrilu 2026, yayin da rikicin Amurka da Iran ke ƙara haddasa fargabar tangarda ga samar da mai a duniya.
Rahoton ya nuna cewa an fitar da lita miliyan 513 na fetur, lita miliyan 534 na dizal da kuma lita miliyan 615 na man jiragen sama cikin watan.
NMDPRA ta bayyana cewa matatar mai mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana da ke Lekki, Jihar Legas, ta yi aiki da kaso 99.12 cikin 100 na ƙarfin ta a watan Afrilu, inda ta kasance babbar matatar da ke samar da mai a Najeriya.
Karanta:Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai
Rahoton ya ce matatar ta samar da kusan lita miliyan 55.4 na mai a kowace rana, tare da fitar da kaso mai yawa zuwa ƙasashen waje duk da buƙatun cikin gida.
Masana harkar mai sun danganta ƙarin buƙatar kayayyakin man Najeriya da rashin tabbas da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar, musamman dangane da tsaron mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.
Rahoton ya kuma nuna cewa Najeriya na ƙara sauyawa daga ƙasar da ke shigo da fetur zuwa cibiyar fitar da mai a Afirka saboda yawaitar samarwar matatar Dangote.
Sai dai duk da ƙarin tace mai a cikin gida, farashin fetur ya ci gaba da tsada a Najeriya, lamarin da NMDPRA ta danganta da tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Recent:NDC ta sanya fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan Naira Miliyan 60
