Daga Sani Adamu Hassan
Wani matashin dan kwallon kafa da ke buga gasar Premier ta Ghana, Dominic Frimpong, ya rasa bayan da ‘yan fashi da makami suka kai hari kan motar tawagarsu yayin dawowar su daga wasa.
Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana (GFA) ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin, tana mai bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga kungiyar Berekum Chelsea da kuma harkar kwallon kafa ta kasar baki ɗaya.
A wata sanarwa da kungiyar Berekum Chelsea FC ta fitar, ta ce wasu mutane dauke da makamai, ciki har da bindigogi masu sarrafa kansu, sun bude wuta kan motar ‘yan wasan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji domin tsira.
Rahotanni daga ‘yan sanda sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na dare a kan hanyar Ahyiresu–Kwame Dwumor Sreso da ke yankin Nyinahin a kudancin jihar Ashanti.
Karanta:Zulum Warns Against Aiding Boko Haram Insurgents
An ce Frimpong ya samu munanan raunuka daga harbin bindiga, inda daga bisani ya mutu a asibiti yayin da ake kokarin ceto rayuwarsa.
Hukumar GFA ta bayyana Frimpong a matsayin matashin dan wasa mai hazaka wanda yake nuna kwazo da jajircewa a wasan kwallon kafa.
Dan wasan mai shekaru 20 ya koma Berekum Chelsea a matsayin aro daga kungiyar Aduana Stars a farkon shekarar nan, inda ya buga wasanni 13 tare da zura kwallaye biyu.
Recent:ADC Inaugurates New Bauchi Leadership, Dankama Pledges Unity, Electoral Repositioning
