Sai da aka yi min tiyata a makogwaro bayan hira da Al Jazeera – Bwala.Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa an yi masa tiyatar makogwaro kwanaki takwas bayan hirarsa da ɗan jaridar Al Jazeera, Mehdi Hasan.
Bwala ya bayyana hakan ne a wani shiri na talabijin, inda ya kuma mayar da martani kan suka da aka yi masa a kafafen sada zumunta bayan hirar.
Ya zargi wasu magoya bayan siyasa da ake kira “Obidients” da fifita biyayya ga shugabansu fiye da muradun ƙasa.
Karanta:APC reshen jihar Kano ta yaba da ziyarar da shugaban jamiyyar na kasa ya kawo
Ya kuma kare yadda ya gudanar da hirar, yana mai cewa tambayoyin Hasan sun kasance irin na ‘yan adawa domin ƙoƙarin ɓata sunan gwamnati, amma bai samu nasara ba.
Hirar dai ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda masu suka suka caccaki Bwala, musamman bayan Hasan ya nuna bidiyoyin tsoffin kalamansa da ya yi wa Tinubu suka kafin ya koma jam’iyyar APC. Haka kuma, an matsa masa kan matsalar tsaro a ƙasar, inda bai gabatar da cikakkun bayanai ba
Recent:2027: NBA ta gargadi lauyoyi da alƙalai kan tsoma baki a harkokin jam’iyyu
