<strong>Jam’iyyar NDC ta sanya kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 kan naira miliyan 60, tare da bayyana cewa za ta yi amfani da tsarin “ɓoyayyen zaɓe a fili” wajen gudanar da zaɓen fidda gwani.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Moses Cleopas, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Abuja, inda ya ce za a fara sayar da fom daga 13 zuwa 18 ga Mayu, 2026.
A cewarsa, masu neman takara za su bi tantancewa tare da gabatar da takardunsu kafin fara sayar da fom ɗin tsayawa takara daga 21 zuwa 23 ga Mayu, yayin da za a rufe karɓar fom da aka cike a ranar 25 ga Mayu.
Karanta:Zaben 2027: NNPP ta tsawaita wa’adin sayen fom din takara
Jam’iyyar ta kuma tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na mukamai daban-daban a ranakun 27 da 28 ga Mayu, yayin da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gudana a Abuja ranar 29 ga Mayu.
NDC ta bayyana cewa masu neman takarar shugaban ƙasa za su biya naira miliyan 20 domin fom ɗin nuna sha’awa da kuma naira miliyan 40 na fom ɗin tsayawa takara, jimilla naira miliyan 60.
Jam’iyyar ta kuma ce mata da masu buƙata ta musamman za su samu rangwamen kaso 50 da 25 cikin ɗari a kuɗaɗen fom ɗin dukkan mukamai.
Recent:Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai
