<strong>Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Bauchi, SUBEB, ta nesanta kanta daga zargin da ake yi na sayar da guraben aikin koyarwa, inda ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu a irin wannan aiki zai fuskanci matakin tsaro.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Isah Jungudo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Bauchi.
karanta:Masu neman takarar gwamnan Yobe a APC sun yi watsi da tsayar da ɗan takara ta maslaha
A cewarsa, hukumar ta samu rahotannin cewa wasu mutane na karɓar kuɗi daga hannun jama’a da sunan samar musu aikin koyarwa a makarantu.
“Ya zo mana da labari cewa wasu marasa kishin ƙasa sun mayar da karɓar kuɗi daga jama’a domin ba su aikin koyarwa tamkar sana’a,” in ji sanarwar.
Jungudo ya jaddada cewa hukumar SUBEB ba ta da wata alaƙa ko hannu a cikin irin waɗannan ayyuka da ya bayyana a matsayin damfara.
haka, Hukumar SUBEB ta Jihar Bauchi ba ta da wata alaƙa da wannan mummunan aiki, saboda haka muna nesanta kanmu daga irin wannan lamari,” ya ƙara da cewa.
Ya kuma buƙaci al’umma da su kai rahoton duk wanda suka gani ko suka ji yana karɓar kuɗi da sunan ɗaukar malamai zuwa ga hukumomin da suka dace.
“Saboda haka muna kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wanda ake zargi da karɓar kuɗi da sunan aikin
koyarwa ga hukumomin da suka dace,” in ji shi.
Hukumar ta kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ɗauki matakan da suka dace domin dakile irin waɗannan ayyuka tare da hukunta masu hannu a ciki.
Recent:Jihohin Nigeriya 18 na iya fuskantar ambaliyan ruwa ~ NiMet
