Jam’iyyar NNPP ta ƙara wa’adin saye da karɓar fom din takara na zaben 2027 da mako guda.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya tuna cewa jam’iyyar ta sanya ranar 10 ga watan Mayu a matsayin ranar fara sayar da fom din takarar.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Comrade Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas ranar Litinin.
Olaposi ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin kwamitin amintattu na jam’iyyar ga kwamitin ƙoli na ƙasa (NWC), wanda ya kafa jam’iyyar, Dr Boniface Aniebonam, ya sanya wa hannu.
Karanta:Amb Yusuf Maitama Tuggar: Miles Away From An Underachiever
Ya ce an ƙara wa’adin ne saboda jinkirin da INEC ke yi wajen ɗora sunayen tabbatattun shugabanin NNPP karkashin Dr Agbo Gilbert Major.
A cewarsa, sabon wa’adin tattarawa da mayar da fom din takara ya koma ranar 17 ga watan Mayu.
Ya ƙara da cewa kudin fom din takarar shugaban ƙasa ya kai Naira miliyan 5, gwamna Naira miliyan 2.5, sanata Naira miliyan 1.5, majalisar wakilai Naira miliyan 1, sannan majalisar dokokin jiha Naira 500,000.
Olaposi ya bukaci masu neman takara da su kwantar da hankalinsu duk da jinkirin da ake samu daga INEC, yana mai tabbatar musu da cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.
