Dandazon magoya bayan Hon. Dr. Adamu Aliyu, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Jos North North a Majalisar Dokokin Jihar Plateau, sun fito domin nuna cikakken goyon bayan su ga jagoran nasu.

An ga magoya bayan sun hallara a harabar Majalisar Dokokin Jihar Plateau dauke da kayan tallafi, tutoci da hotunan ɗan majalisar, yayin da suke bayyana gamsuwa da irin ayyukan ci gaba da wakilcin da yake yi wa al’ummar mazabar.

Wasu daga cikin magoya bayan sun bayyana cewa sun fito ne domin tabbatar da cewa suna tare da Hon. Dr. Adamu Aliyu saboda yadda yake kokarin kawo ci gaba da inganta rayuwar al’umma musamman matasa da mata.
Karanta:Matatar Dangote ta fitar da Lita Biliyan 1.66 na mai a watan Afrilu

An kuma hangi matasa da dama sanye da riguna masu dauke da sunan Hon. Dr. Adamu Aliyu, yayin da wasu ke rera wakokin yabo tare da daga alamar nasara domin nuna farin cikin su.

Masu halartar taron sun bayyana cewa suna fatan ganin cigaban da aka fara zai ci gaba domin amfanin al’ummar Jos North.
Zenith Media – Gaskiya da Riƙon Amana
Recent:2027: Kwankwasiyya ta caccaki Shekarau bisa kalaman sa na zargin Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki
