Kwamitin kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Dattawan Najeriya ya gayyaci tsohon shugaban Nigerian National Petroleum Company Limited, Mele Kyari, domin ya yi bayani kan wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai naira tiriliyan 210 da ake zargin ba a yi cikakken bayanin yadda aka kashe su ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da yake jagorantar kamfanin.
Rahotanni sun ce an gayyaci Kyari tare da tsohon babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan kula da harkokin zuba jari, Bala Wunti, domin su bayyana gaban kwamitin su yi karin bayani kan lamarin.
Shugaban kwamitin, Aliyu Wadada, ne ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin.
Kwamitin ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama waɗanda abin ya shafa idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin a ranar da za a sanar nan gaba.
Karanta:Shuwagabanni marasa kishi ne Matsalar Afirka inji Obasanjo
Sanata Wadada ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani bayan kammala taron kwamitin.
A cewarsa, ana sa ran tsoffin shugabannin kamfanin za su bayyana tare da shugabancin kamfanin na yanzu ƙarƙashin jagorancin sabon Babban Darakta na NNPCL, Bayo Ojulari, da kuma masu binciken kuɗi na waje da suka yi aiki da kamfanin a lokacin da ake magana a kai.
Zenith Media za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da kawo muku karin bayani.
Recent:MAJALISAR KANO TA ƘADDAMAR DA MATAKAN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNA AMINU GWARZO
