Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Plateau ta sake jaddada takunkumin da aka sanya kan zirga-zirgar babura masu zaman kansu da na kasuwanci a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, , ya bayyana takaicinsa kan lalata gonaki da aka yi a yankin Lokojoro tare da kashe shanu a Nding da Kasuwan Dankali da ke Barkin Ladi.
A cewarsa, rundunar tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su tabbatar da aiwatar da dokar cikin tsanaki domin hana sake samun matsalar karya doka da oda.
Karanta:DANDAZON MAGOYA BAYA SUN FITO DOMIN NUNA GOYON BAYAN SU GA HON. DR. ADAMU ALIYU A JOS NORTH
Har ila yau, rundunar ta tunatar da jama’a cewa har yanzu dokar hana zirga-zirgar Keke-Napep a ranar Sallah da washegari tana nan daram. Haka kuma, haramcin baburan kasuwanci a yankin Jos–Bukuru da sauran wuraren da tsarin Jos Greater Master Plan ya shafa na ci gaba da aiki.
Rundunar ta bayyana cewa waɗannan matakai ba don tauye haƙƙin jama’a ba ne, sai dai domin kare rayuka da dukiyoyi da tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
Sai dai rundunar ta ce bincike kan lamarin lalata gonaki da kashe shanun na ci gaba, tare da alƙawarin kamo waɗanda ake zargi domin gurfanar da su a gaban shari’a.
An kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da suka gani mai tayar da hankali ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen hana aikata laifuka a cikin al’umma.
Recent:Bauchi Youth Parliament Adopts Resolutions On Inclusion, Empowerment, Drug Abuse
