Yau, 7 ga Satumba, rana ce mai cike da tarihi da kuma tunawa mai raɗaɗi ga al’ummar JosJos da Jihar Plateau.

A irin wannan rana ta 7 ga Satumba, 2001, rikici ya barke a birnin Jos, wanda daga bisani ya rikide zuwa mummunan tashin hankali da ya yi sanadin asarar rayuka masu yawa, lalata dukiyoyi da raba dubban mutane da muhallansu.

Rikicin na shekarar 2001 ya fara ne a Jos a ranar Juma’a, 7 ga Satumba, sannan ya bazu zuwa sassa daban-daban na birnin. Rahotanni daga Human Rights Watch sun bayyana cewa daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu, yayin da dubban mutane suka rasa matsugunansu cikin kwanakin tashin hankalin.

Abin da ya faru a wancan lokaci ya bar babban gibi a tarihin Jos, tare da haifar da tsoro, rashin zaman lafiya da kuma tabarbarewar dangantakar al’umma.

Yau, bayan shekaru 25, 7 ga Satumba ya zama rana ta tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu, da kuma tunatar da al’umma muhimmancin zaman lafiya, fahimtar juna da kaucewa duk wani abu da zai sake jefa Plateau cikin irin wannan bala’i.
Domin Plateau ita ce “Home of Peace and Tourism” — kuma zaman lafiya ya kamata ya zama gadon da za mu bar wa al’ummomin da ke zuwa.

Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka samu raunuka da waɗanda suka rasa muhallansu haƙuri, kuma Ya tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Plateau da Najeriya baki ɗaya.
Rahoto: Zenith Media
Sake tsarawa: Zenith Media
