<strong>Ƙungiyar Kwankwasiyya ta mayar da martani ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, kan zargin cewa jagoran kungiyar kuma jigo a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, na aiki a boye domin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Zargin dai ya samo asali ne daga wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka rawaito Shekarau yana cewa shi da Kwankwaso na da alaƙa da burin sake zaben Tinubu, ko da yake Kwankwaso na yin hakan a ɓoye. Sai dai Shekarau ya nesanta kansa daga kalaman, yana mai cewa an kirkiri su ne ta hannun masu yada labaran karya.
Rahotanni sun bayyana cewa ba a samu ainihin bidiyon da ake magana a kansa ba, duk da kokarin neman tabbaci daga wasu kafafen yaɗa labarai.
Mai magana da yawun Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mailemo, ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, yana mai cewa ana amfani da irin wadannan maganganu ne don neman farin jini a siyasa. Ya kuma ce Shekarau ya kamata ya rika auna kalamansa kafin ya yi magana a fili, yana gargadin cewa irin wannan na iya rage masa kima a siyasa.
A nasa bangaren, ya ce Kwankwaso mutum ne mai tsayawa kan gaskiya a harkokin siyasa, yana mai cewa ba ya yin siyasa cikin rufa-rufa ko dabara.
Karanta:NDC ta sanya fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan Naira Miliyan 60
Haka kuma ya yi ikirarin cewa Shekarau ya daina taka rawar gani a siyasar Kano, inda ya ce ana amfani da shi ne wajen cimma muradun wasu a siyasa.
A gefe guda, kakakin Shekarau, Farfesa Sule Ya’u Sule, ya musanta kalaman gaba daya, yana mai cewa labarin bogi ne da masu yada karya suka kirkira, tare da cewa Shekarau ba ya Kano lokacin da ake ikirarin an yi maganar.
Ya ce tushen labarin ya fito ne daga wani mai rubutu a kafar intanet, wanda daga baya ya nemi afuwa tare da alkawarin goge shi.
Kwankwasiyya ta ce tana da kwarin gwiwar cewa gaskiya za ta bayyana yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.
Recent:Matatar Dangote ta fitar da Lita Biliyan 1.66 na mai a watan Afrilu
