Hukumar Ilimin Firamare ta jihar Plateau ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu na firamare da na karamar sakandare a fadin jihar nan take.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mr Richard Jonah, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a birnin Jos.
Mr Jonah ya tabbatar wa iyaye, masu kula da yara da sauran masu ruwa da tsaki cewa rufe makarantun mataki ne na ɗan wani lokaci, amma dole ne domin kauce wa yiwuwar barazanar tsaro.
