Bayan sassauta dokar takaitaccen lokaci (curfew) na awanni 48 da Gwamnan Jihar Plateau ya yi, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bassey Ewah, ya shawarci jama’a da su bi dokar yadda aka tsara, yana mai jaddada cewa za a tsaurara matakan tabbatar da bin dokar.
A safiyar yau, wata takaddama da ta faru tsakanin wasu matasa a unguwar Nassarawa Gwong, a karamar hukumar Jos North, ta haifar da ɗan tashin hankali. Abin takaici, wasu bata-gari sun yi amfani da wannan dama wajen tayar da firgici da tsoro tsakanin ‘yan kasuwa da dalibai a yankin jami’a. Sai dai rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro sun gaggauta shiga tsakani, sun shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya.
Haka kuma, an dauki matakai na jigilar dalibai zuwa wuraren da suka zaba, tare da kara yawan jami’an tsaro domin kare sauran dalibai da kadarorin makaranta.
Karanta:MURIC Ta Zargi Caleb Mutfwang Da Nuna Wariya Ga Musulmai
Ya zuwa yanzu, rundunar ta kama mutane bakwai (7) da ake zargi, ciki har da:
Matthew Musa (shekaru 27) wanda aka kama dauke da bindigogi guda biyu na gida
Yakubu Abdullahi (shekaru 26) wanda aka samu sanye da kayan sojoji tare da katin shaidar makarantar sojoji na bogi
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike a Sashen CID na jihar, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Kwamishinan ‘yan sandan ya gargadi duk masu shirin tayar da zaune tsaye cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta su bisa doka. Ya kuma jaddada cewa ba za su bari a mayar da jihar fili na tashin hankali ba.
Daga karshe, ya roki iyaye, shugabannin gargajiya da na addini da su gargadi ‘ya’yansu da mabiyansu su bi dokar curfew, domin rundunar za ta dauki mataki mai tsauri kan duk wanda ya karya doka
Recent:INEC za ta cire sunayen shugabannin ADC bangaren David Mark daga rajistarta
