Daga Mustapha Abdullahi
Ƙungiyar kare hakkin Musulmai ta Najeriya reshen jahar Filato, ta zargi gwamnatin Filato da nunawa wariya ga Musulman jahar yayin jawabin da gwamna Caleb Mutfwang ya yi bayan farmaki da wasu ƴan bindiga suka kai a Anguwar Rukuba.
A cikin wata sanarwa da MURIC ta fitar ta ofishin shugaban ta na Filato Mallam Abubakar Sadiq Yusuf, Ƙungiyar ta ce Gwamnan bai ambaci Musulmai hudu da aka kashe da Musulmai 10 da suka samu rauni ba. Lamarin da MURIC ta ce nuna wariya ne da rashin adalci ga al’ummar musulmi.
“Ya kamata a ce gwamna Caleb Mutfwang ya yi adalci ga kowa ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabilanci ba”
Karanta:Kotu ta soke umarnin sammacin kama Kabiru Turaki a Abuja
Ƙungiyar har wa yau ta yi kira ga hukumomi da su yi bincike domin gano masu hanu cikin tayar da faɗa tare da hukunta su.
Daga ƙarshe, MURIC ta yi kira ga al’ummar jahar Filato da su rungumi zaman lafiya domin da shi ne ake samun dukkan ci gaba mai ɗorewa.
Recent:Gwamna Yusuf ya shaida sauya sheƙar ‘yan majalisar tarayya 8 daga NNPP zuwa APC a majalisar taraiya
