C-JTF NA BUKATAR TAIMAKON GWAMNATI DA MASU HANNUN DA SHUNI A FILATO

Kungiyar Civilian Joint Task Force, C-JTF reshen Jihar Filato, ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro a jihar.
A wani shiri na musamman da aka gudanar ranar Asabar a Jos, an tattara bayanan mambobin ƙungiyar daga ƙananan hukumomin Jos Arewa, Bassa da Mangu domin inganta tsarin gudanarwa.
Kwamandan C-JTF na Jihar Filato kuma Koodinetan ta ƙasa, Tanimu Shehu, ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu zuwa yanzu, inda ƙara da roƙar gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa musu da muhimman kayayyakin aiki.
Ya ce fiye da mambobin dubu hudu na kungiyar a jihar Filato suna shirye su yi aiki tare da hukumomin tsaro idan aka samar musu da kayan aiki da tallafi.
A lokacin da su ke jaddada buƙatar tallafin, Kwamandojin ƙananan hukumomin Bassa da Mangu, Victor Morris Andai da Ismail Usman Muhammad, sun bayyana shirin su na sadaukar da lafiya da ƙarfin su wajen bayar da gudunmawa a harkar tsaro.
Babban kwamandan sashen binciken ƙwaƙwaf na rukunin “BA”, Lukman Auwal Danladi, ya tabbatar da shirye-shiryen su na taimakawa wajen rage matsalar rashin tsaro a jihar Filato da kewaye, yana mai ƙarawa da neman goyon baya da addu’oi daga gurin al’umma baki ɗaya.
Daga ƙarshe kafatanin mambobin ƙungiyar ta C-JTF ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Tanimu Shehu, sun gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da kuma shugabannin C-JTF na ƙasa baki ɗaya, bisa goyon baya, suna masu miƙa ƙoƙon barar su akan neman ƙarin taimako na zahiri daga gwamnati da al’umma, wanda su ka ce hakan ne zai ƙara ƙarfafa aikin ƙungiyar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
