Daga Mustapha Abdullahi
Farashin man fetur a ƙasar Amurka ya haura dala $4 kan kowane galan karo na farko cikin kusan shekaru huɗu, sakamakon rikicin tsaro da ya shafi mashigar ‘Strait of Hormuz’.
Bayanai daga kungiyar masu ababen hawa ta Amurka ‘American Automobile Association’ sun nuna cewa matsakaicin farashin ya kai dala $4.018, daga ƙasa da dala $3 a ƙarshen watan Fabrairu.
Karanta:Bayan ganawa da Kwankwaso a Kano, Gawuna zai yanki katin jam’iyyar ADC a yau Talata
Rahotanni da jaridar Daily Trust ta tattaro sun ce tashin farashin na da alaƙa da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, bayan matakan soja da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ɗauka.
Haka kuma, katsewar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz—wacce ke ɗaukar kusan kashi 20 na man duniya ta ƙara tayar da hankalin kasuwannin makamashi, inda farashin ɗanyen mai ya haura dala $100 kowace ganga.
Recent:Kasashen duniya 10 ne suka amince da jakadun Tinubu, yayin da sauran ke jiran tsammani
