Daga Mustapha Abdullahi
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa aƙalla ƙasashe 10 sun amince da jakadun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, yayin da wasu ke ci gaba da jiran sahalewar ƙasashen da za a tura su.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Kimiebi Ebienfa ne ya bayyana hakan, yana mai cewa har yanzu ana kan aiwatar da matakan samun amincewar sauran ƙasashe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙasashen da suka riga suka amince sun haɗa da Birtaniya, Faransa, Amurka, Ireland, Qatar, Benin, Habasha, Djibouti, Senegal da kuma Saliyo.
Ebienfa ya kuma sanar da cewa jami’an diflomasiyya 19 na Najeriya sun samu karin girma zuwa matsayin jakadu, yana mai cewa za a sanar da ranar bikin rantsar da su bayan kammala shirye-shirye daga fadar shugaban ƙasa.
Recent:Bayan ganawa da Kwankwaso a Kano, Gawuna zai yanki katin jam’iyyar ADC a yau Talata
