A gasar cin kofin zakarun mata ta Turai Real Madrid da Bayern Munich sun samu nasarori masu muhimmanci a wasanninsu na baya-bayan nan.
Kungiyar Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar bayan da ta doke Paris Saint-Germain da ci 2–1 a Paris.
Naomie Feller ce ta fara zura kwallo a raga a minti na 29 bayan kyakkyawan haɗin kai daga Yasmim.
Kafin a tafi hutun rabin lokaci, Alba Redondo ta kara ta biyu bayan kokarin Caroline Weir ya buga sandar raga.
PSG ta rage tazarar ta hannun ‘yar Najeriya Rasheedat Ajibade a minti na 57, amma duk da kai hare-hare da dama, ba su samu daidaita wasan ba.
A wani wasa daban, Bayern Munich ta doke Juventus da ci 2–1 a Jamus.
Pernille Harder ce ta fara zura kwallo, sai dai Eva Schatzer ta daidaita wasan mintuna kaɗan bayan haka.
Amma daga bisani, ‘yar canji Lea Schuller ta zura kwallo ta ƙarshe da ta tabbatar da nasarar Bayern.
Rahotanni sun nune cewa Alba Redondo yanzu ita ce ke kan gaba da kwallaye uku a gasar, yayin da PSG ta sha kashi karo na huɗu a jere, kuma mafi muni tun daga shekarar 2017.
