Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Samata Barau Jibirin da Shugaban kwamitin raya yankin arewa maso yamma suna kiran a kawo wa yankin ɗauki
Sun bayyana hakan ne a taron ci gaban arewa maso yamma, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, inda ‘yan majalisa, masana ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara domin tattauna makomar yankin.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya ce dole ne yankin arewa maso yamma ya sake tsarawa tare da gina ƙarfinsa domin tasiri kan alkiblar tattalin arziƙin Najeriya baki ɗaya.
Sanata Barau ya jaddada cewa hanya mafi inganci ita ce ƙarfafa cibiyoyin yankin da tsarin haɗin gwiwa, maimakon dogaro da tsare-tsaren jihohi daban-daban da ba su da daidaito, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai samar da ci gaba mai ɗorewa a yankin.
