Daniel Asama Ago, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bassa/Jos North Federal Constituency a Jihar Plateau State, ya naɗa Abdulaziz Muhammad Sani a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa (SA Political Matters).
A cikin wata takardar naɗi mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Maris, 2026, Hon. Asama Ago ya sanar da Abdulaziz Muhammad Sani cewa an ba shi wannan muƙami domin ya taimaka wajen tafiyar da harkokin siyasa da kuma hidima ga al’ummar mazabar Bassa/Jos North.
Hon. Asama Ago ya taya sabon mai ba da shawarar murna tare da jaddada cewa ana sa ran zai yi iya ƙoƙarinsa wajen yi wa al’ummar mazabar hidima tare da kare amincewar da aka ba shi ta wannan naɗi.
Har ila yau, a cikin wasiƙar, an buƙaci Abdulaziz Muhammad Sani da ya gabatar da takardar amincewa da naɗin (Letter of Acceptance) cikin makonni biyu daga ranar da ya karɓi wasiƙar.
Wannan naɗi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shugabanni da al’ummar mazabu domin inganta wakilci da ci gaban yankin.
— Zenith Media News
