Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles za ta buga wasan sada-zumunta da takwararta ta Iran, kamar yadda aka shirya. Sai dai batun yaƙin da ake tsakanin Iran da Amurka-Isra’ila zai iya kawo tarnaƙi.
Wasan ƙarshe da Nijeriya da Iran suka buga tsakaninsu shi ne na zagayen rukuni a gasar Kofin Duniya na 2014, inda aka tashi 0-0. / CAFCAF
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta sanar da jerin wasannin sada zumunta da babbar tawagar ƙasar, Super Eagles za ta buga tare da ƙasashe uku da za a fara a watan Maris ɗin nan.
Super Eagles za ta buga wasannin sada zumuntar na gayyata a birnin Amman da ke Jordan. Kuma an shirya buga wasannin lokacin hutun FIFAFIFA na wasannin ƙasa-da-ƙasa na Maris ɗin nan.
Ranar 27 ga Maris Super Eagles za ta buga wasan da takwararta ta Iran, kamar yadda jadawalin wasannin ya nuna. Sai ranar 31 ga Maris, Nijeriya ta kara da Jordan. Sauran ƙasashen biyu su ne Jordan mai masaukin baƙi, da kuma Costa Rica.
Ga Nijeriya, wasannin za su zama na share fagen wasannin neman cancantar buga gasar Kofin ƙasashen Afirka na 2027, inda koci da jami’an wasa za su samu damar tantancewa da zaɓar ‘yanwasa.
Wasannin na zuwa ne yayin da ya rage watanni uku a a fara gasar kofin duniya na FIFA 2026 a ƙasashen Amurka, Mexico, da Canada. Amma a yanzu Nijeriya ba ta cancanci shiga gasar ba.
Karanta:Trump ya yi gargaɗin samun ƙarin mutuwar dakarun Amurka a yaƙin Iran
