Mahaifin margayi Bilyaminu wanda matarsa Maryam Sanda ta halaka, Ahmed Bello Isa, ya ce shi ne ya roki Shugaba Tinubu ya yafe mata bayan yanke mata hukuncin rataya da kotu ta yi.
Ahmed ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jarida, tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda.
- Ya ce dalilin da ya sanya shi rokon kuwa, shi ne don ta rungumi ‘ya’yansu biyu marayu da margayin ya bari, kuma a ganinsa hukuncin kisan da aka yanke mata ba zai dawo masa da dansa ba.
Idan ba amanta ba Arana Asabar daya wuce ne 11 Oct 2025 Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yafewa wasu 175 ciki harda Ita Maryam Sanda. Ga Cikakken labarin
