Daga Mustapha Abdullahi
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan shirin karɓar sabon rance na dala biliyan 6, tana mai gargadin cewa hakan na ƙara jefa Najeriya cikin matsalar bashi.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mailemo ya fitar.
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar rancen ne domin cike giɓin kasafin kuɗi da aiwatar da ayyukan more rayuwa.
Karanta:INEC za ta cire sunayen shugabannin ADC bangaren David Mark daga rajistarta
Sai dai kakakin ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya ce amincewa da irin waɗannan rance ba tare da cikakken nazari ba na barazana ga tattalin arzikin ƙasa, yana mai zargin cewa ana iya karkatar da rabon kuɗaɗen zuwa wasu yankuna.
Ya kuma soki Majalisar Ƙasa bisa zargin gazawa wajen sa ido kan ɓangaren zartarwa, yana mai cewa hakan na raunana dimokuraɗiyya.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta dakatar da karɓar bashi ba tare da tsari ba tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen amfani da albarkatu.
