ƙungiyar APC ta yi gargaɗi ga Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Nentawe
Wata ƙungiya a cikin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, mai suna Renewed Hope Advocates of Nigeria (RHAN), ta yi gargaɗi ga Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Yilwatda Nentawe, da kada ya bari ƙiyayyarsa ga Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang ta lalata shi a siyasance.
RHAN wadda kuma ƙungiya ce mai goyon bayan Tinubu a cikin jam’iyyar, ta kuma lura cewa ƙiyayyar Nentawe ga Mutfwang na iya jefa damar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 cikin haɗari a jihar.”’
