Binciken Rundunar soja ya gano wasu kudi Naira Biliyan N45 da aka raba daga Asusun ajiyar hukumar raya yankin Niger Delta, zuwa ga wasu mutane da ke da alaka da siyasa, da kuma sojojin da aka tsare bisa zargin hadin baki wajen yunkurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Rahotanni da dama a ranar Talata sun baiyana cewa, Sojoji sun kai samame a gidan tsohon Gwamna kuma tsohon Ministan man fetur Timipre Sylva, bisa zargin alaka da yunkurin juyin mulkin, da sashin tara bayanan sirri na rundunar Sojin ke bincike a kai.
Biyo bayan wannan bankada, masu bincike daga sashin tara bayanan sirri na soji, sun titsiye wasu manyan jami’an hukumar NDDC game da hanyoyin fitar kudaden, wadanda suka ci gajiyar su, da kuma yadda aka raba su.
A yayin da babu cikakkun bayanai kan titsiyen da aka yi wa jami’an na hukumar NDDC, ance masu binciken na bibiyar fitar kudade a jere cikin watannin nan, da ake zargin na da alaka da wasu ‘yan Siyasa.
Sun hada da wata kwangila da aka ba wa tsohon Gwamna a kudu maso kudu, da ta kai ta Naira Biliyan N45, wasu daga cikin kudaden da aka yi zargin sun yi batan dabo a Asusun jami’an sojan da ake tsare da su.
