Daga Sani Adamu Hassan
Jigo a jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, Dr. Ladan Salihu Ilelah, ya soki Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, kan abin da ya kira tsoma bakin da ake yi a harkokin shugabanci na jam’iyyar.
A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Trust, Dakta Ilelah ya bayyana cewa, “Abin mamaki ne yadda INEC ke bayar da umarni wajen dakatar da shugabancin jam’iyyar mu, abin kunya ne.”
Ya zargi hukumar da yin aiki ba tare da jiran cikakken tsarin shari’a ba, inda ya ce, “INEC ta yi riga malam masallaci; bai kamata ta fitar da wata sanarwa ba tukuna saboda ‘yan Najeriya sun san waye shugabannin ADC, babu wanda ya san wancan.”
Dr. Ilelah ya kara da cewa, “INEC tana nuna goyon baya ga jam’iyyar APC,” yayin da ya bayyana cewa sauyin sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa ADC ya canza yanayin siyasar Najeriya, wanda hakan ya sa jam’iyyar gwamnati cikin rudani da damuwa kan zaben 2027.
karanta:Bankin Duniya ya amince da rancen dala miliyan 500 domin tallafa wa ƙananan manoma a Najeriya.
Ya ce, “Sun jefa dukkan dabaru da salon siyasa na boye-boye domin raunana, rushe, da rage karfin ADC. Amma hakan ba zai yi aiki ba. ‘Yan Najeriya na da hakkin samun zaɓi daban, dandali daban, da damar siyasa daban – shi ne dimokuradiyya.”
Har ila yau, Dr. Ilelah ya gargadi hukuma, inda ya ce, “Hukumar shari’a kada a ga tana cikin haɗin guiwa da kowace jam’iyya, ko APC ma, wajen raunana tsarin dimokuradiyya.”
A karshe, ya jaddada bukatar INEC ta kasance da gaskiya, ba tare da nuna wariya ba, tare da bin doka da ka’idoji, yana mai cewa hukumar kada ta dauki kanta a matsayin mai tsaka-tsaki da kuma mai shiga wasa a lokaci guda, kamar yadda Albarka Radio ta rawaito.
Recent:Kotun daukaka kara ta haramta wa hukumar NBC cin tarar gidajen rediyo da talabijin a Nijeriya
