Daga Sani Adamu Hassan
Bayanai sun ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara tun ƙarfe 2:30 na dare zuwa 11:30 na safiyar jiya Asabar ne ya yi sanadin ambaliyar da ta zowa jama’a da ba zata.
Ko da yake saukar ruwan saman ya samar da sauƙin tsananin zafin da aka kwashe tsahon makonni ana yi a yankunan, amma kuma ya zo da barna mai yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta shafi unguwannin Mile Six, Mafindi da kuma Mayogwai, sai kuma babbar kasuwar Jaligo da ruwan ya shafe shaguna.
Karanta:Bauchi Govt Commissions New Public Health Laboratory To Boost Disease Control
Mazauna yankunan da ambaliyar ta fi yiwa illa sun shaidawa manema labarai cewa ambaliyar ta faru ne a sakamakon toshewwar magudanan ruwa, ganin yadda ruwan ya zo a bazata, kasancewar lokacin faɗuwar damuna a yankunan bai yi ba.
Bayanai sun nuna cewa ambaliyar ta kuma haddasa cunkoson ababen hawa a kan babbar hanyar Jalingo zuwa Wukari sakamakon yadda ta haɗu da aikin sabuwar gada da ake ginawa.
Wannan shine karo na biyu cikin makonni uku da ruwan sama ke dakatar da aikin ginin gadar.
