Daga Mustapha Abdullahi
Rundunar Yansanda a Jihar Ogun ta ce jami’an ta sun cafke wasu mutane uku bisa zargin kisan wani mutum mai suna Stanley Okirie mai kimanin shekaru 38 a yankin Akute, karamar hukumar Ifo.
Wadanda aka kama sun hada da Maureen Okirie mai shekaru 35, Salia Karikari mai shekaru 15, da Jubril Karikari mai shekaru 12.
karanta:TROOPS NEUTRALIZE TERRORISTS, RECOVER ARMS IN PLATEAU
Jaridar Punch ta rawaito cewa rahotanni sun nuna cewa an kashe Okirie ne sakamakon duka da tabarya, inda kuma ana shirin binne gawarsa a ɓoye ne sai jami’an ƴansanda su ka samu bayanan sirri, sai suka kai samame su ka kuma dakile shirin tare da kama waɗanda ake zargi.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar, DSP Oluseyi Babaseyi, ya bayyana cewa an samu nasarar kwato makamin da ake zargin an yi amfani da shi wajen kisan, sannan an kai gawar mutuware ta Life Channel Mortuary da ke Olambe domin gudanar da binciken gawar.
Ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano cikakken yadda abin ya faru da kuma hukunta masu hannu a ciki.
