Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Ministan Yaɗa labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan harin saman da rundunar sojin sama ta kai a kasuwar Jilli da ke ƙaramar hukumar Gubio a jihar Borno.
Rahotanni sun ce harin ya auku ne a ranar Lahadi, inda ya afkawa kasuwar da ke tsakanin Gubio da Geidam, ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama tare da jikkata wasu. Amnesty International ta yi iƙirarin cewa sama da mutane 100 sun mutu, sai dai rundunar soji ta ce an nufi harin ga ‘yan Boko Haram ne.
A cikin wata sanarwa, Ministan ya ce binciken zai duba yadda aka samu bayanan sirri, da yadda aka zaɓi wurin d aka kai harin, da yadda aka aiwatar da aikin, tare da tabbatar da ɗaukar mataki idan an samu kura-kurai.
karanta:Barau da Abdullahi Abbas sun nuna buƙatar a baiwa Bichi mataimakin gwamnan Kano
Ya ƙara da cewa duk da cewa harin ya ta’allaka ne kan bayanan sirri domin raunana ‘yan ta’adda, gwamnati na takaicin duk wani asarar rayukan fararen hula, tana mai jaddada cewa rayuwar kowane ɗan ƙasa na da muhimmanci.
Haka kuma, ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin jihohin Borno da Yobe da kuma hukumar agajin gaggawa ta ƙasa domin kai agajin jin ƙai ga waɗanda abin ya shafa.
Recent:JOS YOUTH INITIATIVE FORUM REJECTS HON. DANIEL ASAMA AGO FOR SECOND TERM
