Tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma, ya yaba wa Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa abin da ya bayyana a matsayin jan hankalin duniya kan matsalar tsaro da kashe-kashe da ke addabard yankin Middle Belt na Najeriya.
Danjuma ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 2026, jim kaษan bayan da aka ba shi digirin girmamawa na Digirin Digirgir (Honoris Causa) a Jamiโar Jihar Filato da ke Bokkos, Jihar Filato, yayin bikin yaye ษalibai karo na 8 da na 9 da aka gudanar a haษe.
A cewarsa, kalaman Trump kan halin da ake ciki a yankin, musamman game da barazanar da ke fuskantar alโummomin Middle Belt, sun sanya sunan yankin ya zama sananne a faษin duniya.
Ya ce kafofin yaษa labarai na ฦasa da ฦasa sun mayar da hankali kan batun, inda mutane da dama suka nuna mamaki, wasu kuma suka rikice, amma duk da haka tattaunawar ta ci gaba.
โYau, duniya tana sauraron gaskiyar yankinmu da kyau,โ in ji shi.
Danjuma ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin ci gaba, yana mai cewa hakan ya ฦara fito da matsalolin da yankin ke fuskanta tsawon shekaru, ciki har da rikice-rikicen manoma da makiyaya, kashe-kashe, da yawaitar gudun hijira.
Ya jaddada bukatar daukar matakai na gaggawa domin kawo ฦarshen tashin hankalin da ke ci gaba da addabar yankin, tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ga alโummomin Middle Belt.
