A yayin da ake ce-ce-ku-ce game da kwato motocin gwamnati daga kwamishinonin da suka yi murabus a gwamnatin Abba Kabir Yusuf suka bi Sanata Kwankwaso, jam’iyyar NNPP ta bankado yadda aka siyarwa da Muhyi Magaji Rimin Gado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, motocin hukumar a kuɗaɗe kalilan.
Mai magana da yawun NNPP na riko na jihar Kano, Engr. Ibrahim Karaye ne ya wallafa takardar cinikayyar a shafin sa Facebook, wacce DAILY NIGERIAN HAUSA ta gani.
A cikin takardar mai dauke da kwanan watan 19/8/2025 an ga gwamnati ta siyarwa da Muhyi mota kirar Toyota Corolla ,kan Naira 425,000 kacal, inda kuma aka siyar masa da Nissan Hillux kan kuɗi N833,333.33 shi ne ya hada jimilla Naira Miliyan 1 da dubu 258,333.33.
Karanta:Iran ta watsar da damarta ta shiga yarjejeniyar sulhu – Trump
A sakon da ya wallafa, mai magana da yawun jam’iyyar ta NNPP ya sha alwashin bankado irin badakalar da gwamnatin ke aikatawa daga yanzu.
Recent:Charging booth operator killed as Lakurawa terrorists raid Sokoto village
