Wasu masu neman takarar gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyyar APC guda shida sun yi watsi da batun tsayar da ɗan takara ta hanyar maslaha gabanin zaɓen 2027, inda suka buƙaci a gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, masu neman takarar sun ce yunƙurin kakabawa jam’iyyar ɗan takara ba tare da bin tanade-tanaden kundin tsarin APC da dokar zaɓe ba zai iya haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar a jihar.
Cikin masu neman takarar akwai tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba; Sanatan Yobe ta Kudu, Ibrahim Bomai; tsohon shugaban hukumar NEMA, Mustapha Maihaja; da wasu manyan jiga-jigan APC.
Rahotanni sun ce Gwamna Mai Mala Buni da wasu shugabannin APC sun nuna goyon baya ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Baba Wali, a matsayin wanda suke so ya gaje shi.
Masu neman takarar sun bayyana cewa idan ba a samu sahihin matsaya ta maslaha tsakanin dukkan ‘yan takara ba, to ya kamata APC ta gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani kai tsaye domin bai wa mambobin jam’iyyar damar zaɓar wanda suke so.
Haka kuma sun zargi shugaban APC na jihar Yobe, Mohammed Gadaka, da nuna bangaranci, inda suka ce sun rasa amincewa da shi wajen gudanar da zaɓen fidda gwani cikin adalci.
Sai dai duk da korafe-korafen nasu, sun sake tabbatar da biyayyarsu ga APC tare da nuna goyon baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙudirin sake zaɓensa a 2027.
Recent:Gwamnatin Oyo ta hana sayar da raguna a manyan tituna lokacin babbar Sallah
