Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a harkokin siyasa, , ya fito ya bayyana matsayinsa kan rade-radin da ke yawo dangane da makomar siyasarsa da kuma rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce har yanzu bai dauki wata cikakkiyar shawara ba kan makomar siyasarsa ko ta mabiyansa, yana mai jaddada cewa rahotannin da ke cewa yana shirin sauya akala ba su da tushe.
“No final decision has been taken regarding my political future or that of my political associates.”
Ya bayyana cewa duk da hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da sahihancin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar karkashin jagorancin David Mark, amma batun ya koma kotun koli ta jiha, lamarin da ya jefa jam’iyyar cikin rudani.
Hakazalika, ya nuna damuwa kan hukuncin Kotun Tarayya da ya soke taron gangamin jam’iyyar da aka yi, tare da matakin da Babban Lauyan Tarayya ya dauka na neman a soke rajistar ADC gaba daya.
Karanta:Ina nan a kan matsayina na takarar Sanata babu gudu babu ja da baya-Yusuf Zailani
Kwankwaso ya kara da cewa sun bar jam’iyyar NNPP ne sakamakon matsalolin shari’a da suka shafi tasirin waje, kuma yanzu haka ADC ma na fuskantar irin wannan kalubale.
“We have commenced wide-ranging consultations… to explore the best options for protecting our democratic interests.”
Ya bayyana cewa suna tuntubar manyan masu ruwa da tsaki daga jam’iyyu daban-daban ciki har da NDC da PRP domin gano mafita mafi dacewa.
Dangane da batun takarar shugaban kasa, Kwankwaso ya ce bai bayyana aniyarsa ba, kuma bai goyi bayan kowane dan takara ba, yana mai cewa duk wani rahoto da ke cewa haka ba gaskiya ba ne.
“I have neither declared any intention to run for president nor endorsed any aspirant.”
Ya kuma yi karin haske cewa rashin halartar sa a wasu tarukan jam’iyyar ADC na baya-bayan nan ya samo asali ne daga wasu uzurori na kashin kai da ba za a iya kauce musu ba, wanda ya ce ya sanar da shugabannin jam’iyyar tun da wuri.
A karshe, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da tuntuba da muhawara kafin daukar kowace muhimmiyar shawara, tare da alkawarin sanar da jama’a matsayinsu a hukumance da zarar lokaci ya yi.
Recent:Kwankwaso Na Duba Yiwuwar Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar NDC
