Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya kaddamar da rabon kayan koyarwa da na karatu ga makarantun firamare a fadin kananan hukumomi 17 na jihar, domin inganta ilimi da bunkasa koyarwa a makarantu.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a hedikwatar Plateau State Universal Basic Education Board (SUBEB) da ke Dogon Dutse a Jos, inda gwamnan ya kuma kaddamar da sabon ginin ofisoshin hukumar tare da duba ayyukan da aka aiwatar.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar farfado da ilimin gwamnati a Plateau, yana mai cewa idan ba a gyara ilimin gwamnati ba, ba za a iya cewa ilimi ya inganta a jihar ba.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa tana aiki kan gina sabbin ajujuwa, horar da malamai, da samar da kayan koyarwa domin dawo da martabar ilimi a jihar.

A wajen taron, an kuma karrama wasu dalibai da suka daga martabar jihar a gasar wasannin makarantu ta kasa da aka gudanar a Bauchi.
Karanta:Gobara ta ƙone Cocin St. Mary’s Catholic Cathedral da ke garin Wukari a Jihar Taraba.
Shugaban SUBEB na jihar, Sunday Amuna, ya ce hukumar ta gina ajujuwa 397, ta gyara 557, tare da hako rijiyoyin burtsatse 33 domin samar da ruwa ga makarantu.
Hakazalika, gwamnatin jihar ta raba littattafai 143,931, jakunkunan makaranta 6,675, takalman makaranta 6,675, tare da kayan rubutu domin tallafawa dalibai da malamai a makarantun firamare.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shiri wani bangare ne na kokarin gwamnati na inganta ingancin ilimi da karfafa tsarin koyarwa a jihar Plateau.
— Zenith Media News
Recent:NSCDC, ‘yan sanda da sojoji sun kama mutane 99 a samame a Ondo.
