Darakta hulɗa da jama’a na Diocese Katolika na Wukari, Rev. Fr. John Laikei, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne jim kaɗan bayan dawowar wutar lantarki a yankin.

Karanta:Gwamnatin Plateau Ta Naɗa Kwamitin Rabon Tallafin Ramadan da Sallah 2026
Rahotanni sun ce wutar ta lalata rufin ginin da kayayyakin da ke cikin cocin gaba ɗaya. Sai dai babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

Wannan na zuwa ne watanni kaɗan bayan wata gobara ta lalata sakatariyar Karamar Hukumar Wukari.
Recent:Jarumin Kannywood Haruna Talle Maifata Ya Musanta Zargin Rashin Bai Wa ‘Yan Jos Shinkafa
