Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta ce wani samame na hadin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar a ranar Lahadi ya kai ga kama mutane 99 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassan jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin a birnin Akure.
Jimoh ya ce wannan aiki na hadin gwiwa ya hada da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo, rundunar 32 Brigade Artillery ta Sojojin Najeriya, da kuma rundunar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) ta jihar Ondo.
Ya kara da cewa sauran hukumomin tsaron da suka shiga aikin sun hada da Department of State Services (DSS) da kuma Hukumar Tsaron Jihar Ondo (Amotekun Corps).A cewarsa,
“An gudanar da wannan aiki ne bisa bayanan sirri inda aka kai samame wuraren da ake zargin maboyar masu aikata laifi ne, da wuraren da ake yawan aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar.
“Wannan aiki na hadin gwiwa ya kai ga kama mutane 99 da ake dangantawa da laifuka kamar fashi da makami, fasa gidaje, sata, kungiyar asiri (cultism), da sauran laifuka makamantansu.
“Har ila yau, a yayin samamen an kwato kayayyaki da dama da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka, da kuma wasu dukiyoyi da ake zargin an sace tare da sauran kayayyakin da za su iya zama hujja.”
Ya ce a halin yanzu ana tantance wadanda aka kama tare da tattara bayanansu, sannan duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Jimoh ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adebowale Lawal, ya yaba da kwarewa, hadin kai da jajircewar jami’an tsaron da suka shiga wannan aiki.
A cewarsa, kwamishinan ya jaddada cewa irin wannan hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen yakar laifuka a jihar.
Har ila yau, ya sake nanata kudurin rundunar na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri da hadin gwiwar hukumomi domin rushe kungiyoyin masu aikata laifi da kuma tabbatar da doka da oda a jihar.
Karanta:Gwamnatin Plateau Ta Naɗa Kwamitin Rabon Tallafin Ramadan da Sallah 2026
“Lawal ya sake gargadin masu aikata laifi da su daina aikata haramtattun ayyuka a cikin jihar, yana mai jaddada cewa Jihar Ondo ba za ta zama mafakar masu laifi ba.
“Hukumomin tsaro za su ci gaba da kara kaimi wajen gano, bibiyar, da hukunta masu aikata laifi duk inda suke ko inda suka boye.”
Don haka ya bukaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba su sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen yaki da laifuka.
Recent:Gobara ta ƙone Cocin St. Mary’s Catholic Cathedral da ke garin Wukari a Jihar Taraba.
