Wani gagarumin biki na nuna al’adu da ya bayyana haɗin kai da ɗimbin wadatar al’adun Najeriya ne ya fi ɗaukar hankalin jama’a a bikin Makon Ɗalibai na 2025 na Skyline School of Health Technology, Jos, inda malamai da ɗalibai suka hadu waje guda domin karfafa zaman lafiya, haɗin kai, da soyayya ta hanyar waƙoƙi, rawa, da nune-nunen gargajiya.
An gudanar da wannan mako na musamman daga ranar Laraba, 22 zuwa Lahadi, 26 ga watan Oktoban 2025, inda aka shirya abubuwa daban-daban kamar zaben sabbin shugabannin kungiyar dalibai (SUG), wasa da wasannin motsa jiki, kwalliya da rigunan ƴan ƙwallo (jersey carnival), tare da balaguron ilimi zuwa Jos Wildlife Park da Asibitin Plateau Specialist Hospital, Jos.
A yayin bikin nuna al’adun, ɗalibai sun wakilci ƙabilu daban-daban irin su Hausa, Igbo, Yoruba, Afizere, da Fulani, inda suka fito cikin ƙayatattun kayayyakin gargajiya, wakoki, rawa, da abincin gargajiya, cikin yanayin hadin kai da farin ciki.
An shirya wannan taro ne domin karfafa girmamawa, soyayya, da fahimtar juna tsakanin kabilun Najeriya masu bambancin harshe da al’adu.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Sashen Harkokin Dalibai na makarantar, Malam Haruna Umar, ya jaddada muhimmancin hadin kai a matsayin ginshiƙi na zaman lafiya da ci gaba.
Ya ce, “Karfinmu a matsayimmu na ‘yan kasa yana cikin bambancinmu. Idan muka koyi murna da al’adun juna kuma muka zauna lafiya, to muna kara tura kasar mu gaba.”
Malam Umar ya yaba da rawar da malamai da dalibai suka taka wajen gudanar da Makon cikin nasara, yana mai cewa irin wadannan ayyuka na taimaka wa matasa wajen gina kwarewa a jagoranci, kirkire-kirkire, da hadin kai a cikin al’umma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kammala bikin Makon Dalibai na 2025 na Skyline cikin farin ciki da nishadi, tare da sabunta kudurin ci gaba da gina makaranta mai cike da hadin kai da zaman lafiya.
