Tsohon abokin wasansa, Segun Odegbami, ne ya tabbatar da rasuwarsa a wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar Asabar.
Odegbami ya ce Nwosu ya rasu da misalin ƙarfe 4:00 na safiyar Asabar a asibitin koyarwa na jami’ar Lagos , bayan shafe kwanaki biyar yana jinya a sashen kulawa ta musamman.
Karanta:TINUBU YA BUKACI KAFAFEN YAƊA LABARAI SU SA IDO KAN KUDADEN JIHOHI DA KANANAN HUKUMOMI
Marigayin ya kasance cikin tawagar Najeriya da ta lashe kofin 1980 na gasar kofin Afrika , wanda shi ne karo na farko da Najeriya ta lashe gasar.
A lokacin da yake taka leda, Nwosu ya buga wa Najeriya wasanni kusan 60, sannan ya taka leda a kungiyoyi kamar New Nigeria Bank F.C. da Stationery Stores F.C.. Bayan ya yi ritaya daga wasa, ya koma aikin horaswa da bunƙasa matasan ‘yan wasa.
Recent:Za a sake gurfanar da Sule Lamido kan zargin badakalar Naira biliyan 1.3
