Daga Mustapha Abdullahi
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja ranar 1 ga Afrilu, 2026, bisa zargin badakalar kuɗi har Naira biliyan 1.3 kamar yadda shafin hukumar EFCC ya wallafa.
Za a gurfanar da Lamido tare da ’ya’yansa biyu, Aminu Lamido da Mustapha Lamido, da kuma kamfanoninsu biyu, Bamaina Holdings Ltd da Speeds International Ltd, kan zargin karɓar cin hanci da bayar da kwangiloli na bogi a lokacin da yake gwamna tsakanin 2007 zuwa 2015.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga Afrilu bayan waɗanda ake tuhuma ba su halarci kotu ba a ranar da aka fara sa ran a gurfanar da su, wato 13 ga Maris, 2026.
Tun da farko, Kotun Ƙoli a ranar 16 ga Janairu, 2026 ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta wanke su, tare da umartar a ci gaba da shari’ar a babbar kotun tarayya.
Recent:TINUBU YA BUKACI KAFAFEN YAƊA LABARAI SU SA IDO KAN KUDADEN JIHOHI DA KANANAN HUKUMOMI
