Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kafafen yaɗa labarai a ƙasar nan da su ƙara sanya ido kan yadda gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ke tafiyar da kuɗaɗen da suke karɓa, kamar yadda suke bibiyar kuɗaɗen gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin mallaka kafafen yaɗa labarai da manyan editoci a fadarsa ta Aso Rock Presidential Villa da ke Abuja.
Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun bai wa ƙananan hukumomi damar karɓar kuɗaɗensu kai tsaye, wanda a cewarsa zai taimaka wajen ƙara inganta ayyukan ci gaba a matakin ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa jihohi na samun ƙarin kuɗaɗen shiga sakamakon ingantaccen tsarin tattara haraji da kuma ƙaruwa a samar da ɗanyen mai.
Shugaban ƙasar ya jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da kuɗaɗen gwamnati a dukkan matakan mulki.
— Zenith Media News
