Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Dakarun Operation Whirl Stroke sun kama wani babban wanda ake zargi da aikata laifi a ƙauyen Agasha da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue, bayan wani rahoton kai hari kan wani mazaunin yankin.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, wadda Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, mukaddashin jami’in yaɗa labarai na hedikwatar rundunar JTF Operation Whirl Stroke, ya sanya wa hannu, rundunar haɗin gwiwar ta bayyana cewa an ƙaddamar da wannan samame ne a ranar 13 ga Maris, 2026, bayan samun sahihan bayanai kan harin da aka kai wa Mista Shaapera Seeta Michael.
Sanarwar ta ce:
“Da samun rahoton, dakarun Chief of Army Staff Intervention Battalion XI da aka tura ƙarƙashin Operation Whirl Stroke sun yi gaggawar tashi zuwa yankin domin gano wanda ake zargi da aikata harin.”
Da isar su wurin, dakarun sun kewaye yankin domin hana wanda ake zargin tserewa, yayin da suka fara bincike na musamman domin gano tare da kama wanda ake zargin.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“An samu nasarar kama wanda ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar ‘yan sa-kai mai suna Suurnen David Akum, mai shekaru 27, ɗan ƙauyen Agasha a ƙaramar hukumar Guma. Haka kuma an kwato wani bindiga da aka ƙera a gida daga hannunsa yayin kamun.”
Ta ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin kafin a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki na gaba.
Karanta:Za a sake gurfanar da Sule Lamido kan zargin badakalar Naira biliyan 1.3
Kwamandan rundunar Joint Task Force Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Moses Gara, ya yaba wa dakarun kan ƙwarewa da dabarun da suka nuna, wanda ya kai ga samun nasarar kama wanda ake zargin.
Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da ƙoƙari tare da kasancewa cikin shiri domin hana masu aikata laifi samun damar gudanar da ayyukansu a yankin.
Recent:Yau ake sanar da mutuwar Tsohon dan wasan Najeriya Henry Nwosu
