Gwamnatin Jihar Plateau ta sanar da naɗin kwamitin wucin-gadi da zai kula da rabon kayan abinci na tallafin Ramadan da Sallah na shekarar 2026 ga al’ummar Musulmi a faɗin jihar.
A cikin sanarwar da aka fitar, Gwamnan jihar, Caleb Manasseh Mutfwang ya ce naɗin kwamitin na daga cikin manufofin gwamnatinsa na tabbatar da jin daɗin al’umma da tallafawa marasa ƙarfi musamman a lokacin azumin Ramadan.
Karanta:Akwai yiyuwar mutum 2 sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Adamawa
An naɗa Rt. Hon. Abubakar Kanam daga Ƙaramar Hukumar Kanam a matsayin Shugaban Kwamitin.
Sauran membobin kwamitin sun haɗa da:
Hajiya Jamila Wase – Ƙaramar Hukumar Wase
Bello Danjuma – Ƙaramar Hukumar Quan Pan
Adamu Dauda – Ƙaramar Hukumar Riyom
Abdullahi Yakubu – Ƙaramar Hukumar Jos North
Jibril Lawal Usman – Ƙaramar Hukumar Jos North
Alhaji Saleh Abdullahi Zazzaga – Ƙaramar Hukumar Jos South
Ahmed Mohammed Inuwa – Ƙaramar Hukumar Shendam
Alhaji Safianu Adamu – Ƙaramar Hukumar Bokkos
Alhaji Salisu Akuba – Ƙaramar Hukumar Mangu
Haka kuma, an naɗa Alhaji Yusuf Abdullahi Wase a matsayin Sakataren Kwamitin.
Gwamnan ya umarci kwamitin da su tabbatar an tsara rabon tallafin cikin gaskiya da adalci a dukkan ƙananan hukumomin jihar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko wata akida ba.
Sanarwar ta kuma yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun al’umma tare da kawo zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Plateau.
— Zenith Media News
Recent :Sen.Buba Inaugurates Islamic Scholars’ Centre In Bauchi, Donates N20m To Health College Project
