Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a Jihar Jigawa ta kama wani tsohon shugaban ɗalibai (Prefect) bisa zargin ƙoƙarin satar kayan dakin gwaje-gwaje na makaranta a Dutse.
Mai magana da yawun rundunar NSCDC a Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya tabbatar da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse ranar Alhamis.
Wanda ake zargin, Aliyu Musa, mai shekaru 22, jami’an NSCDC sun kama shi ne bayan korafi daga mahukuntan makarantar kan yawaitar sace kayan dakin gwaje-gwaje.
Tijjani ya ce, “Wanda ake zargin, wanda a baya shi ne Labour Prefect na makarantar, an kama shi ne yayin da yake ƙoƙarin ɗauke microscopes guda biyar daga babban dakin gwaje-gwajen makarantar.”
Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa a baya ma wasu kayan dakin gwaje-gwaje sun ɓace, ciki har da conical flasks guda 10, microscopes guda 10 da sauran kayayyaki.
Ya ce, “Matakin gaggawa da jami’an NSCDC suka ɗauka ya hana ci gaba da lalata da satar muhimman kayan aikin ilimi.”
Mai magana da yawun ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da tura jami’ai tare da ƙara sa ido a makarantu domin hana ayyukan laifi.
A cewarsa, an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa laifin shiga harabar makaranta ba tare da izini ba da kuma sata domin a gurfanar da shi a gaban shari’a.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro domin hana duk wani abu da zai kawo cikas ga harkar ilimi.
Sannan ya bukaci mazauna jihar da su rika sanar da jami’an tsaro mafi kusa da su duk wani abu da ya basu shakku a kusa da makarantu.
Karanta:Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun dakile wani hari da mayaƙan ISWAP
Rundunar NSCDC ta Jihar Jigawa ta kuma sake jaddada cewa shirin Safe School an kirkiro shi ne domin kare makarantu da muhimman kayayyakin more rayuwa.
Tijjani ya kuma bayyana cewa kwamandan NSCDC na jihar ya gargadi masu niyyar aikata laifi da su nisanci makarantu a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, “Rundunar za ta ci gaba da aiki tare da mahukuntan makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ingantaccen yanayin koyo mai aminci.”
Recent:Gwamnan Plateau Ya Kaddamar da Gyaran Matatar Ruwa ta Yelwa,
