Ya Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Sama da Naira Biliyan 28 don Inganta Ruwan Sha
Caleb Manasseh Mutfwang, Gwamnan Plateau State, ya kaddamar da matatar ruwa ta Yelwa Water Treatment Plant bayan kammala aikin gyaranta, tare da sanya hannu kan yarjejeniyar da ta haura Naira biliyan 28 domin inganta tsarin samar da ruwan sha a jihar.

An gudanar da wannan biki ne a wani bangare na bukukuwan cika shekaru 61 na gwamnan, inda ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na kokarin gwamnatinsa wajen samar da tsaftataccen ruwa mai dorewa ga al’ummar Bukuru, Gyel da sauran yankunan da ke kewaye.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, Gwamna Mutfwang ya gode wa Allah tare da cewa farin cikin jama’a shi ne babbar kyauta da ya samu a ranar haihuwarsa.
Ya ce babu wata kyauta da ta fi sanya farin ciki a zuciyarsa kamar ganin murmushi a fuskar al’umma, musamman mata da ke yawan fuskantar wahalar nemo ruwa domin amfanin gida.
Gwamnan ya jaddada cewa duk da cewa jihar Plateau na da wadataccen ruwa a dabi’a, babban kalubalen da ake fuskanta shi ne tsaftacewa da kuma rarraba ruwan yadda ya kamata zuwa gidajen jama’a.
Ya kuma gargadi jami’an da ke kula da harkar ruwa da su tabbatar da kulawa da kayan aiki yadda ya dace domin kaucewa barazanar lafiyar jama’a.
Haka kuma, gwamnan ya yi gargadi kan gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba a kusa da tafkuna da wuraren ajiye ruwa, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani ci gaba da ka iya kawo barazana ga kayan aikin samar da ruwa ba.

Tun da fari, Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Makamashi na jihar, Lawandi Datti, ya bayyana cewa gyaran matatar ruwan ta Yelwa babban mataki ne na dawo da ingantaccen ruwan sha ga al’ummar yankin.
Ya ce aikin zai kara samuwar ruwa, inganta tsafta da lafiyar jama’a, tare da rage matsalolin da ke tattare da rashin wadataccen ruwa.
A nasa jawabin, Matthew Verghis ya yaba da sauyin da aka samu a cibiyar, yana mai cewa gyaran da aka yi zai taimaka matuka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

A wani bangare na kokarin kara inganta harkar ruwa a jihar, Gwamna Mutfwang ya kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanonin kasar Sin, wato China Geo-Engineering Corporation da Shanxi Construction Investment Group.
Karanta:Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15, Sun Jikkata Da Dama A Katsina
Za a aiwatar da aikin ne da tallafin rance daga French Development Agency, inda ake sa ran aikin zai mayar da hankali kan gyaran da fadada cibiyoyin tsaftace ruwa da hanyoyin rarraba ruwa domin magance matsalar ruwa da aka dade ana fama da ita.
Gwamnan ya kara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen kara wadatar ruwa a birnin Jos tare da sabunta tsofaffin kayan aikin da aka girka tun shekarun 1970.
A cewarsa, wasu daga cikin injinan da ke Laminga Dam an girka su tun kusan shekarar 1973 zuwa 1974, kuma suna yawan lalacewa tare da cin makamashi mai yawa, don haka sabon aikin zai kuma maye gurbin tsofaffin bututun ruwa da suka lalace a sassan birnin.
Ana sa ran wannan shiri zai inganta samar da ruwan sha, karfafa tsarin rarraba ruwa, da kuma tabbatar da samun tsaftataccen ruwa ga al’ummar jihar Plateau.
Recent:Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun dakile wani hari da mayaƙan ISWAP
