Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto kuma Sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa ADC, inda ya danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan wata 11 ga watan Maris, 2026, da ya aika wa shugaban PDP na mazabarsa a Tambuwal/Shinfiri na ƙaramar hukumar Tambuwal.
Karanta:CG AUDI YA INGANTA DOKAR TSARON DAN ADAM A AIKIN NSCDC
Takardar, wadda aka bai wa manema labarai, ta bayyana cewa matakin barin PDP ya biyo bayan shawarwari da ya yi da abokan siyasa da magoya bayansa.
Recent:Ranar Mata ta Duniya: ‘Yan sanda sun bai wa zawarawan jami’an da suka rasu kayan abinci a Jigawa.
