Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya tana kan irin tsarin samar da ci gaba ga ‘yan ƙasar kamar yadda Birtaniya ke kai.
Tinubu ya faɗi hakan ne a lokacin da yake jawabi a Windsor Castle yayin wata ziyara da yake yi a Birtaniya domin amsa gayyatar Sarki Charles.
Ya jinjina wa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya na tsawon lokaci, inda ya nuna jin daɗinsa kan irin karramawar da aka masa a matsayin shugaban Najeriya na farko da ya yi jawabi a Windsor bayan shafe sama da shekaru 40 babu wani shugaban ƙasar da ya taɓa samun irin wannan gayyata.
Karanta:Jos North Chairman Flags Off Construction of Two Primary Healthcare Clinics
“Manufofin Najeriya da Birtaniya suna kamanceceniya da juna ta fuskar samar da ci gaba. Muna fatan inganta alaƙar mu da manufofi iri ɗaya,” in ji Tinubu.
Shugaban Najeriyar ya kuma gode wa Birtaniya kan yadda ta ba shi mafaka a lokacin da suke gwagwarmayar tabbatar da dimokradiyya a ƙasar shekar sama da 20 da suka wuce.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da ke zaune a Birtaniya da su kasance ‘yan ƙasa na gari ta hanyar nuna kyawawan ɗabi’u tare da fatan zumuncin kasashen biyu ya ci gaba da ɗorewa..
