Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara matakan tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin aikata wasu laifuka da suka haɗa da amfani da iko ba daidai ba da kuma cin amanar ƙasa.
Matakin ya fara ne a ranar Alhamis bayan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya gabatar da takardar sanarwar tsigewar a zauren majalisar.

A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne bisa tanadin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa gyara.
Dala ya bayyana cewa takardar tsigewar ta ƙunshi zarge-zarge da dama da suka shafi lokacin da Aminu Abdussalam Gwarzo ya riƙe muƙamin Kwamishinan Kananan Hukumomi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, da kuma matsayinsa na yanzu a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.
Sai dai har zuwa yanzu ba a ji martanin Mataimakin Gwamnan kan waɗannan zarge-zarge ba.
Zenith Media
Recent:Shuwagabanni marasa kishi ne Matsalar Afirka inji Obasanjo
