Daga Mustapha Abdullahi
Shugaban yankin na Church of Christ in Nations (COCIN), Rev. Ezekiel Dachomo, ya mayar da martani ga zargin da wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu, ya yi masa, inda ya ce ya taɓa zama ɗan fashi da makami kuma yana da hannu a wani fashin banki a Jos a shekarar 1980.
A cikin wani mummunan suka da ya bazu sosai, Baban Chinedu ya ce Rev.Dachomo ba wai kawai ɗan fashi mai haɗari ba ne, har ma makaryaci ne da ya ƙirƙiri labarin haɗuwarsa da Yesu Almasihu, kuma ya mayar da kansa mutum mai anfani da rikice-rikice domin samun riba ta hanyar haddasa tashin hankali a Jihar Filato da Arewa baki ɗaya.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a kafafen sada zumunta, malamin addinin Musuluncin ya ce:
“Rev. Ezekiel Dachomo ba wai kawai mutum ne da aka gani a hoto tare da ‘yan bindiga ba; a’a, shi ne ɗan bindigar! Ezekiel ya aikata fashi da makami.
Muna da bayanai a kansa tun daga 1976, daga 1976 har zuwa bayan shekara ta 2000.
Wannan mutum ƙwararren ɗan fashi ne mai hatsari.
Makaryaci ne da ya ƙirƙiri labarin cewa ya haɗu da Yesu bayan wani fashin banki da aka yi a Jos a shekarar 1980.”
Recent:One-Party System Dangerous As Parties Face Crisis In Nigeria, Bauchi –Says Abubakar Kari
